An yi garkuwa da wani lauya mai kare Saddam Hussein | Labarai | DW | 21.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi garkuwa da wani lauya mai kare Saddam Hussein

An yi garkuwa da wani lauya mai kare tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein a shari´ar da ake masa. Kamar yadda ´yan sanda suka nunar wasu mutane da ba´a gane su ba suka kutsa cikin ofishin lauyan a birnin Bagadaza inda suka yi awon gaba da shi da kuma wasu ma´aikatansa su 7. A ranar laraba da ta wuce aka fara zaman sauraron shari´ar da ake yiwa tsohon shugaban na Iraqi. A wani labarin kuma an sako wakilin jaridar The Guardian ta Birtaniya da aka yi garkuwa da shi a ranar laraba. Kamar yadda jaridar ta nunar wasu mazauna birnin Bagadaza suka ceto shi daga hannun wasu ´yan banga.