An yi garkuwa da wani Bajamushe a tarayyar Nijeriya | Labarai | DW | 03.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi garkuwa da wani Bajamushe a tarayyar Nijeriya

Ma´aikatar harkokin wajen Jamus na binciken wasu rahotanni dake nuni da yin garkuwa da wani Bajamushe ma´aikacin wani kamfanin gine-gine. Wata mai magana da yawon ma´aikatar ta ce ana tuntubar ofishin jakadancin Jamus a Abuja da kuma reshensa dake Legas. Rahotanni daga birnin Fatakwal na jihar Rivers sun ce wasu mutane a cikin kayan sarki suka sace mutumin, ma´aikacin kamfanin samar da gas na Bilfinger Berger wato reshen kamfanin gine-gine na Julius Berger.´Yan sanda a Fatakwal sun nunar da cewa an fid da mutumin ne da karfi daga cikin motarsa sannan aka yi awon gaba da shi. Hare hare akan tashoshi da bututun mai da yin garkuwa da ma´aikatan mai ya zama ruwan dare a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir a kudancin Nijeriya.