1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi ganawar farko tsakanin Lauran Bagbo da Charles Konnan banny

Yahouza SadissouDecember 6, 2005

Shugaban kasar Cote D´Ivoire ya sa hannu a kan dokar amincewa da Charles Konnan Banny a matsayin saban Praminista

https://p.dw.com/p/Bu3d
Hoto: AP

Shugaban kasar Cote D´Ivoire Lauran Bagbo ya sa hannu a kan dokar amincewa da nada Charles Konnan banny a matsayin saban praminista.

Magabatan 2, sun yi ganawar farko ta keke da keke a yammacin jiya a birnin Abidjan.

A nasa gefe tsofan Praminista Saidu Diara, ya gabatar da takardar sa ta murabus ga shugaban kasa, ya kuma bukaci wanda ya cenje sa ya kama aiki ba da bata lokaci ba.

Charles Konnan Banny, ya share shekaru da dama a matsayin shugaban babbar bankin kasashen yammacin Afrika.

Ya kuma samu kaukyawar shaida, daga al´ummar kasa baki daya.

A sakamakon kimar da ke gare shi a idon jama´a ba da wata wata ba, shugaba Lauran Bagbo, da jam´iyun adawa da yan tawaye su ka amince da nadin da a ka yi masa.

Mahiman batutuwan da ke rubuce a ajendar ayyukan da za shi zartas sun kunshi shirya zaben shugaban kasa nan da watani 10 masu zuwa, da kuma, kwance damara yakin yan tawaye da ta dakarun sa kai masu goyan bayan Lauran Bagbo.

A jawabin da yayi jim kadan, ganawar sa da Shugaban kasa, Charkes Konnan banny yayi alkawarin cima wannan guri tare da goyan bayan al´umar kasar Cote D´Ivoire, mussamman kungiyoyin fara hulla da na siyasa da kuma yan tawaye.

Yayi kira ga jama´a baki daya, da su da ta ba shi hadin kai, ya yi zabarin kasar daga halin da ta tsinci kanta, tun shekara ta 2002.

Masu kula da harakokin siyasa, na hangen cewa,cimma wannan buri, na kamar wuya ta la´akari da matsanciyar gaba da kyamar juna, da su ka shiga tsakanin bangarorin dabandaban.

Bugu da kari, wani abun da zai iya sa tarnaki ga cimma wannan nasara, shine cikkaken mulki da Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia ya bukaci,a damkawa saban Praministan.

Wannan mataki babu shakka, a cewar su ,a aikace zai fuskanci adawa daga shugaban kasa Lauran Bagbo, da a ke ganin cewar ba za shi taba amincewa ba ya kasance shugaban kasar je ka nayi ka.

Sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi annan, ya aika takardar taya al´umar kasar Cote D´Ivoire murnar kaiwa ga wannan mataki, mai mahimanci a yunkurin samar da zama lahia.

Ya tabara da cewa majalisar da ya ke jagoranta a shire ta ke, ta bi sau da kaffa diddikin al´ammura da za su wakana zuwa gaba, don tabatar da kowa ya cika alkawarin da ya dauka.

Ya kuma bukaci saban Praministan ya zabi mutane kurraru daga bangarori daban daban domin girka gwamnati da za ta aiki na gaskiya, bisa tsarin da kungiyar Afrika da kuma Majalisar Dinkin Dunia su ka cimma daidaito.