1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi ga Amirka da ta tattauna kai tsaye da Iran

April 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1i

Wani fitaccen dan majalisar dattijan Amirka mai fada a ji kuma dan jam´iyar Republican ya ce kamata yayi gwamnatin shugaba Bush ta tattauna kai tsaye da Iran a game da shirinta na nukiliya. Richard Lugar shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin waje ya ce za´a cimma abubuwa masu alfanu idan aka gudanar da wannan tattaunawa kai tsaye. Sinatan ya ce lokaci bai yi ba da za´a matsa lamba don kakabawa Iran takunkumi. Har ya zuwa yanzu gwamnati Amirka na adawa da zama kan teburin shawarwari guda da Iran. Wadannan kalaman na Lugar sun zo ne bayan gargadin da sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta yi cewa dole ne Kwamitin Sulhun MDD ya yi nazari dukkkan matakan da suka wajaba a dauka don jan kunnen Iran. An ba wa kasar wa´adin na da karshen wannan wata da ta dakatar da shirin ta na nukiliya ko kuma a sanya mata takunkumi.