1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi dauki ba dadi tsakanin matasa da sojojin Birtaniya a Basra

May 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuzN

A yau an harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojin Birtaniya a birnin Basra dake kudancin Iraqi, inda aka halaka dukkan sojoji 4 dake cikin jirgin saman. Hakan dai ya janyo arangama tsakanin dakarun Birtaniya da matasan dake jifarsu da duwatsu da kuma bama-baman fetir. Ko da yake har yanzu gwamnatin Birtaniya ta ce ba ta san musabbabin faduwar jirgin ba, amma ´yan sanda a Basra sun ce an harbo jirgin saman mai saukar unugulu ne da wani makami mai linzami. Jirgin ya fadi ne akan wani gida amma ba wanda ya rasa ransa a kasa. Amma majiyoyin ´yan sanda da jami´an tsaro sun ce akalla ´yan Iraqi biyu ko biyar sun rasu sakamakon yamutsin da ya biyo bayan hadarin. Matasan dai sun yi ta rera wakoki na ta ya baradan kungiyar Mehdi murnar nasarar harbo jirgin saman. Ita dai kungiyar wadda ta kunshi ´yan shi´a ta kasance mai adawa da mamayen sojojin ketare a kasar Iraqi. Yanzu haka dai an kafa dokar hana fitan dare a birnin na Basra.