An yi bukin ratsad da sabon Firaministan Japan a birnin Tokyo | Labarai | DW | 26.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi bukin ratsad da sabon Firaministan Japan a birnin Tokyo

An rantsad da sabon FM Japan Yasuo Fukuda a wani buki da aka yi a birnin Tokyo. Fukuda ya yi alkawarin sake daga mutuncin ´yan siyasa a idanun jama´a sannan ya ce zai hada kai da masu adawa da shirin kara wa´adin sojojin ruwan Japan a cikin rundunar kasa da kasa a Afghanistan. Fukuda mai shekaru 71 ya yi kaurin suna wajen sasantawa da ´yan adawa kuma ana daukar sa a matsayin shugaban da Japan ke bukata a yanzu bayan dambaruwar siyasa da ta yi da ita karakshin tsohon FM Shinzo Abe wanda ba zato ba tsammani ya yi murabus makonni biyu da suka wuce. A wani lokaci yau Fukuda da sauran ministocin sa zasu yi ganawarsu ta farko.