1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi bukin rantsad da shugaba Museveni a Kampala

May 12, 2006
https://p.dw.com/p/Buye

Shubaga Yoweri Museveni na Uganda ya zargi kasashen waje da laifin tsoma baki a harkokin siyasar kasar sa. Museveni ya ce hakan ba abin karbuwa ba ne. Shugaban ya yi wannan zargi ne a wajen bukin rantsad da shi don yin sabon wa´adin mulki karo na 3 yau a birnin Kampala. Bayan an rantsad da shi a gaban dubban magoya baya da wasu shugabannin Afirka, Museveni ya zargi kasashe masu ba da rance da masu fafatukar kare muhalli da kuma wasu da ya kira ´yan ketare da hannu a wahalhalun da Uganda ke fuskanta yanzu. Shugaban ya ce sayar da ´yancin kasar wani babban kuskure ne saboda haka ya tabbatarwa ´yan uganda cewa ba za´a taba tabka wannan kuskure ba. Museveni, wanda ke kan mulki har tsawon shejaru 21, shi ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan fabrairu da gagarumin rinjaye. Shugaban ´yan adawa Kizza Besigye wanda ke fuskantar shari´a bisa zargin cin amanar kasa, bai halarci wurin bukin ba.