An yi batakashi tsakanin sojin Turkiya da ´yan tawayen Kurdawa | Labarai | DW | 23.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi batakashi tsakanin sojin Turkiya da ´yan tawayen Kurdawa

Dakarun tsaron Turkiya sun kashe mutane 8 dukkan su ´ya´yan haramtacciyar kungiyar nan ta Kurdawa wato PKK. Jami´an tsaron Turkiya sun ce an kashe mutane a jerin fafatawar da ake yi baya bayan nan a yankunan tsaunuka dake kudu maso gabashin kasar. An halaka mutanen ne a lardin Hakkari dake kusa da kan iyaka da Iraqi, inda gwamnatin birnin Ankara ke zargin cewa maboyar ´yan tawayen kungiyar PKK ne. A cikin watannin baya bayan nan dai an kashe sojojin Turkiya da dama da kuma ´yan tawayen PKK a batakashi da ake yi musamman a yankin Kurdawa na kudu maso gabashin Turkiya. Hakan dai ya kacibis da jerin hare hare da aka kaiwa birnin Istanbul.