An yi barazanar hallaka ´yan Denmark a ketare | Labarai | DW | 05.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi barazanar hallaka ´yan Denmark a ketare

Wata kungiya a Iraqi dake da alaka da Al-Qaida ta yi barazanar kai hare hare akan kadarorin kasashen Turai inda aka buga zane-zanen na sifata Annabi Mohammad SAW. Kungiyar ta kuma yi barazanar halaka ´yan kasar Denmark ta hanyar yi musu gunduwa gunduwa. A cikin wani sako da ta buga ta intanat kungiyar al-Mujahideen ta umarci ´ya´yanta da su kame ´yan kasar Denmark kuma su yi musu yankar rago a duk inda suka hadu da su. Hakazalika kungiyar ta yi kira ga al´umar musulmi da su kauracewa sayen kayakin kasashen da jaridun su suka buga zane-zanen. Shi kuwa ministan harkokin wajen Denmark Per Stig Möller ya fadawa wani taron manema labarai a birnin Kopenhagen cewa ba wanda zai yi nasara a rikicin da ake yi game da zane-zanen.