An yi ba ta kashi tsakanin ’yan Taliban da sojojin NATO a Afghanistan. | Labarai | DW | 20.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi ba ta kashi tsakanin ’yan Taliban da sojojin NATO a Afghanistan.

A Afghanistan, an yi wani mummunan ba ta kashi tsakanin mayaƙan ƙungiyar Taliban da dakarun ƙasar da kuma na ƙungiyar NATO a yankunan kudancin ƙasar, inda rahotanni ke nuna cewa ’yan Taliban 71 da kuma sojojin Afghanistan 5 ne suka rasa rayukansu. An dai yi fafatawar ne a lardin Panjwayi da ke kudancin jihar Kandahar.

A halin da ake ciki dai, ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya fara wata ziyarar kwana 3 a Afghanistan ɗin. Tun cikin watan Yuni ne Jamus, wadda ke da dakaru dubu 2 da ɗari 8 girke a Afghanistan, ta karɓi jagorancin rundunar NATO a arewacin ƙasar.