An yi arangama tsakanin ´yan sanda da masu bore a Kathmandu | Labarai | DW | 21.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi arangama tsakanin ´yan sanda da masu bore a Kathmandu

´Yan sanda a Kathmandu babban birnin kasar Nepal sun kame masu zanga-zanga kimanin 300 lokacin da suka hallara a wajen wani taron gangamin neman karin demukiradiya da jam´iyun siyasar kasar suka kira don bijirewa haramta wannan taro da hukuma ta yi. ´Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar wadanda ke rera wakoki kuma suna jifar ´yan sanda da duwatsu. Jam´iyun na neman sarki Gyanendra da ya maido da mulkin demukiradiya shekara daya bayan ya sallami gwamnati. Matakin murkushe masu zanga-zanga da kame kame da sarkin ya sa ana yi yana shan suka daga MDD, tarayyar Turai, Amirka da kuma Indiya. Sarkin ya ce ya dauki wannan mataki ne don murkushe wani boren ´yan tawaye.