1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi alkawarin ba Pakistan dala miliyan dubu 5.4 a matsayin taimakon sake gina arewacin kasar

November 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvKQ

Makonni 6 bayan mummunar girgizar kasar da ta auku a arewacin Pakistan kasashen duniya masu ba da tallafi sun yi alkwarin ba da taimako da ya kai dala miliyan dubu 5.4. FM Pakistan Shaukat Aziz ya sanar da haka a wajen babban taron kasashe masu ba da tallafi a Islamabad babban birnin Pakistan. Bankin duniya da kuma bankin raya kasashen yankin Asiya sun yi alkawarin ba da dala miliyan dubu daya kowanen su. Pakistan dai ta kiyasce cewar zata bukaci dala miliyan dubu 5.2 don taimakawa wadanda girgizar kasar ta rutsa da su da aikin sake farfado da yankunan da girgizar ta yiwa barna. A wajen bude taron babban sakataren MDD Kofi Annan ya sake yin kira ga kasashen duniya da su cika alkawarin da su ka dauka na ba Pakistan taimako musamman yanzu da sanyin hunturu ke karatowa a yankin na Himalaya.