1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yankewa wasu mutane uku kai a Saudi Arabi´a

December 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvFf

Ma´aikatar kula da al´asmurran cikin gida ta saudi Arabia tace an yankewa wasu mutane uku kawunan su bisa laifuffuka iri daban daban da suka aikata.

A cewar ma´aikatar harkokin cikin gidan, an aiwatar da wannan hukuncin ne a babban birnin kasar wato Riyad a yau talata .

Wadan nan mutane dai sun hadar da Sulaiman bin saad al Shataan da Hassan Bin Mohd al mashi da kuma Tamer Bin Salem, wadan da dukkannin su aka same su da laifin kisan mutane yan uwan su.

Ya zuwa yanzu jumlar mutanen da aka sare musu kann a kasar ta Saudi Arabia daga farkon wannan shekara izuwa yanzu ya tasamma mutane 81.

Rahotanni dai daga kasar sun nunar da cewa hukuncu hukunce dake da nasaba da gille kai,wadanda suka shafi kisan kai da safarar miyagun kwayoyi da fyade da fashi da makami duk ana aiwatar dasu ne da takobi a kuma bayyanar jama´a don hakan ya zama darasi ga yan baya.