1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yankewa wani fada hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a Legas

Wata kotu a birnin Legas ta yankewa wani mai wa´azi na Kirista hukuncin kisa ta hanyar ratayewa bayan ta same shi da laifin zubawa wasu ´yan cocinsa su 7 fetir kana ya cinna musu wuta, inda ya kashe mutum daya. Emeka Ezeuko wanda ´yan cocinsa ke yi masa lakabi da Reverend King, ya musanta jerin zargi guda 6 da aka yi masa. Ya ce mutanen sun kone ne lokacin da wani jenerato ya yi bindiga. Masu shigar da kara da shaidu sun ce Ezeuko ya ci zarafin mutanen a gidansa dake Legas inda ya tilasta musu amsa cewa sun yi zina, sannan sai ya cunna musu wuta a matsayin hukuncin wannan laifi da suka yi. Wani da ya shaida zaman kotun ya ce Ezeuko ya fadawa kotun cewa ba ya tsoron a rataye shi domin an taba rataye annabi Issah.