An yankewa tsohon Firaministan Ukraine hukuncin daurin shekaru 9 a gidan maza | Labarai | DW | 26.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yankewa tsohon Firaministan Ukraine hukuncin daurin shekaru 9 a gidan maza

Wata kotu a jihar Kalifornia ta Amirka ta yankewa tsohon FM Ukarine Pavel Lazarenko hukuncin daurin shekaru 9 a kurkuku bayan ta same shi da laifin yin rub da ciki da kudin kasa tare da halatta kudaden haramun da kuma cin hanci da rashawa. Bugu da kari kotun ta kuma ci shi tarar dala miliyan 10. Lazarenko wanda cikin dare daya ya zama hanshakin miloniya a lokacin da ya rike mukamin FM Ukraine daga 1996 zuwa 1997 ya shiga hannun hukumomin Amirka jim kadan bayan isar sa kasar a 1999. Ya na da hannayen jari sannan kuma ya tara kudaden haramun a kamfanoni da bankuna na kasashe da dama ciki har da Ukraine, Switzerland da kuma Amirka.