An yankewa sojin Amirka hukuncin ɗaurin shekaru 110 bisa laifin fyaɗe | Labarai | DW | 05.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yankewa sojin Amirka hukuncin ɗaurin shekaru 110 bisa laifin fyaɗe

An yankewa wani sojin Amirka da aka same shi da laifin fyade da kuma kisan wata yarinya ´yar Iraqi mai shekaru 14, hukuncin daurin shekaru 110 a kurkuku. Wata kotun soji a Kentucky ta kasar Amirka ta yanke wannan hukunci ga Jesse Spielman mai shekaru 23 bayan an same shi da laifin yin fyade da hada baki don yin fyade da kuma wasu caje caje guda hudu na aikata kisan kai. Ko da ya ke masu shigar da kara na soji ba su ce ko Spielman ya aikata fyaden ba amma sun ce ya je gidan yarinya kuma ya san abin da abokan aikinsa ke da niyar aikatawa sannan ya kasance dan kallo. A cikin watan maris na shekara ta 2006 aka aikata wannan laifi a garin Mahmudiya mai nisan kilomita 20 kudu da birnin Bagadaza.