An yankewa mutum daya da ya saura a garkuwar birnin Beslan hukuncin daurin rai da rai | Labarai | DW | 26.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yankewa mutum daya da ya saura a garkuwar birnin Beslan hukuncin daurin rai da rai

Shekara daya da rabi bayan mummunar garkuwar da aka yi da ´yan makaranta a garin Beslan wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 331, wata kotu a Rasha ta yankewa dan tawaye daya da ya tsira da ransa, hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku. Da farko babbar kotu a yankin Vladikawkas ta ba da shawarar yankewa mutumin hukuncin kisa amma saboda an soke hukunci kisa a Rasha, sai aka sauya wannan hukunci zuwa na daurin rai da rai. Kwanaki 10 da suka wuce kotun ta samu dan tawayen mai shekaru 25 daga yankin Chechniya da laifin yin garkuwa tare da kisan daruruwan mutane. Kotun ta bayyana garkuwar da aka yi a makarantar firamaren ta Beslan da cewa aiki ne na ta´addanci.