An yankewa limamin krista hukuncin daurin shekaru 15 a Rwanda | Labarai | DW | 13.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yankewa limamin krista hukuncin daurin shekaru 15 a Rwanda

Kotun sauraron laifuffukan yaki ta mdd dake Rwanda ,zartar da hukunci kann wani Limamin krista na Roman Katholika ,adangane da samunsa da hannu a kisan kiyashin kasar da akayi a shekarata 1994.Father Athanase Seromba,na mai zama limamin Krista na farko da aka gurfanar tare da yanke masa hukunci na daurin shekaru 15 a gidan kurkuku.An samu Father Seromba dan kabilar hutu,da laifin bada umurnin rusa churchin ,inda wasu yan kabilar tutsi 2,000 suka nemi mafaka a watan Afrilun 1994,inda rusa ginin akansu yayi sanadiyyar mutuwansu baki daya.