An yankewa Fujimori ɗaurin shekaru shida a gidan kaso | Labarai | DW | 12.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yankewa Fujimori ɗaurin shekaru shida a gidan kaso

Wata kotu a ƙasar Peru ta yankewa tsohon shugaban ƙasar Alberto Fujimori hukuncin ɗaurin shekaru shida a kurkuku bisa laifin fatali da dokokin ƙasa. Kotu ta same shi da laifin ba da umarnin yin wani haramtaccen samame a wani gida mallakin matar daya daga cikin jami´an leƙen asirin sa wato Vladimir Montesinos a cikin watan nuwamban shekara ta 2000. Wannan hukunci shi ne na farko da yankewa tsohon shugaban wanda kuma ya ke fuskantar caje caje na keta hakin bil Adama da cin hanci da rashawa. Hukuncin zai kawo masa cikas na kariya a wata shari´a daban ta kisan kai. Fujimori ya shugabancin ƙasar Peru daga shekarar 1990 zuwa 2000 kafin ya tsere zuwa Japan lokacin da gwamnatinsa ta rushe.