An yankewa dan adawar Masar Aiman Nur hukuncin dauri a kurkuku | Labarai | DW | 24.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yankewa dan adawar Masar Aiman Nur hukuncin dauri a kurkuku

An yankewa dan adawar kasar Masar Aiman Nur hukuncin daurin shekaru 5 a gidan maza. An same shi da laifin shirya takardun boge lokacin da ya kafa jam´iyarsa ta Ghad ta masu sassaucin ra´ayi. An gudanar da zanga-zangar nuna adawa da wannan hukunci a ciki da kuma wajen kotun da ta yi zaman sauraron shari´a a birnin Alkahira. A cikin watan satumba Nur ya kasance babban wanda ya kalubalancin shugaba Hosni Mubarak a zaben da aka gudanar a kasar wanda kamar yadda aka sa rai shugaba Mobarak ya lashe. Don nuna adawa da tsare shi a farkon wannan wata na desamba Nur ya fara yajin kin cin abinci a gidan wakafi.