An yanke wa wani ma’aikacin gidan waya hukuncin ɗauri na shekaru 8 a gidan yari, a ƙasar Indonesiya. | Labarai | DW | 07.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yanke wa wani ma’aikacin gidan waya hukuncin ɗauri na shekaru 8 a gidan yari, a ƙasar Indonesiya.

Wata kotu a ƙasar Indonesiya, ta yanke wa wani ma’aikacin gidan waya hukuncin ɗaurin shekaru 8 a gidan yari, saboda samunsa da laifin da ta yi, na kasancewa ɗaya daga cikin masu shirya harin ƙunan baƙin waken nan da aka kai a kan tsibirin Bali, a shekarar bara. Da yake yanke hukuncin, babban alƙalin kotun, Wayan Rena Wardana, ya ce babu shakka an tabbatar cewa mutumin da ake tuhumar, Dwi Widyarto, mai shekaru 33 da haihuwa, na da hannu a cikin ayyukan ta’addancin da aka gudanar. Harin da aka kai a ran 1 ga watan Oktoban shekarar bara, a kan tsibirin Balin dai, ya janyo asarar rayukan mutane 20, abin da ake gani kuma kamar cikas ne ga yunƙurin farfaɗo da tattalin arzikin tsibirin, bayan harin shekara ta 2002, inda masu yawon shaƙatawa fiye da ɗari 2 suka rasa rayukansu.

A ran talatar da ta wuce ma, sai da kotun ta yanke wa wani malamain makaranta, Abdul Aziz, mai shekaru 30 da haihuwa, hukuncin ɗauri na shekaru 8 a gidan yari, shi ma saboda samunsa da laifin da aka yi na taka muhimmiyar rawar gani a wannan harin.