1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN YANKE HUKUNCIN ZARGIN DA AKEWA SHUGABAN YAN ADAWA A ZIMBAWE:

October 15, 2004
https://p.dw.com/p/BvfW

Wata babbar kotu a birnin Harare na kasar Zimbabwe tza yanke hukuncin wanke shugaban yan adawa na jamiyyar MDC,wato Morgan Changirai daga laifin da ake zargin sa da aikatawa.

A can baya dai an zargi Changirai da laifin shirya makarkashiya ta kifar da gwamnatin shugaba Robert Mugabe a hannu daya kuma da aikewa dashi lahira babu shiri.

A cikin sanarwar hukuncin da kotun ta bayar ta nunar da cewa Morgan Changirai bashi da wani laifi bisa wadan nan zarge zarge da gwamnatin kasar ta Zimbabbwe tayi masa.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa jim kadan bayan yanke wan nan hukunci daga bakin babban jojin kotun wato Padddington Garwe,magoya bayan madugun yan adawar suka kaure da tafi da guda don nuna farin cikin su game da wan nan hukunci.

A lokacin da yake karanta hukuncin wanke changirai,babban jojin kotun wato Paddington,wanda ya shafe awa daya da minti 20 yana karantawa ya tabbatar da cewa babu kanshin gaskiya a cikin wadan nan zarge zarge guda biyu da akewa Morgan Changirai ba ko kuma inda Ari Ben Menashe ya taimakawa Changirai wajen aiwatar da kisan Robert Mugabe ba.

Bugu da karo jojin ya kuma shaidar da cewa babu koja Ari Benm menashe yayi kokarin shigar da Changirai cikin wan nan laifin ne bayan daya karbi masu gidan rana,a don haka shi ba wanda zai bayar da shaida bane a yarda da ita.

Bayanai dai sun tabbatar da cewa anyi arangama a tsakanin magoya bayan Morgan Changrai din da kuma jamiasn yan sanda a wajen kotun,a kokarin da yan sandan keyi na tarwatsa taron mabiya jamiyyar ta MDC dake gudanar da bukukuwan murna na wanke shugaban nasu daga wadan nan laifuffuka biyu na sama da muka ambata.

A cewar mataimakin shugaban jamiyyar ta MDC wato Gibson Sibanda,cewa yayi wan nan hukunci da babbar kotun kasar ta yanke ya nunar a fili cewa har yanzu alkalai a kasar na rike da mutuncin su wajen tabbbatarwa da mai gaskiya gaskiya tare da bawa mai laifi laifi.

A yanzu haka dai magoya bayan jamiyyar ta MDC da kuma shugaban adawar wato Morgan Changirai na can na gudanar da bukukuwan jin dadin wan nan hukunci da aka yanke,wanda aka shafe kusan shekara daya anayi,musanmamma bisa laakari da cewa akwai hasashen cewa kutun ka iya tabbatar da laifuffukan da ake zargin Changirai da aikatawa.

Matukar kuwa aka samu haka a cewar rahotannin da suika iso mana Morgan Changirai zai fuskanci hukuncin kisa ne ba tare da bata wani lokaci ba.

A can baya dai gwamnatin shugaba Robert Mugabe ta zargi Morgan Changirai da shirya makarkashiyar kisan Shugaba Mugabe tare da taimakon wani dan kasar Canada dake gudanar da aikin sa kai a kasar dake da suna Ari Ben Menashe.

Gamsassun bayanai dai sun shaidar a fili cewa Ari Ben Menashe ya karbi tsabar kudi na dalar Amurka har dubu dari 650 don shirya wan nan kinibibi a kann shugaban yan adawar kasar ta Zimbabbwe.

Bisa hakan ne Ari Ben Menashe ya zama na sahun gaba wajen bayar da shaidar karya na tsunduma Morgan Changirai a cikin laifi a tsawon lokacin da aka dauka ana gudanar da wan nan sharia.

Ibrahim Sani.