An yanke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe dan jarida a Sudan | Labarai | DW | 10.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yanke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe dan jarida a Sudan

A ƙasar Sudan an yankewa mutane 10 hukuncin kisa bisa laifin kisan tare da fille kan wani ɗan jarida mai ra’ayin islama a 2006.Cikin tsauraran matakan tsaro Alakali a kotun Bahri a birnin Khartoum ya sanarda wannan hukunci,bayan watanni 9 ana sauraron shari’ar.

Mutanen waɗanda suka fito daga kabilar Fur daga lardin Darfur an kama su ne da laifin kashe Muhammad Taha babban editan wata jaridar islama ta Al wifaq.

Rahotanni dai sun ce Ahmed yana da danganta mai tsami da gwamnatin Al Bashir yayinda kuma yake ɓata ran yan tawayen Darfur da irin rubuce rubucen da yake yi yana sukar su.

Bisa dokokin Sudan ana yanke aiwatar da hukuncin kisa ne ta hanyar ratayewa amma kuma mutum yana da damar ɗaukaka kara