1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yanke hukunci a shari'ar Al-Tawhid

October 26, 2005

Wata kotu a Düsseldorf ta yanke hukunci akan wasu da ake zargi da kasancewa 'ya ta'adda

https://p.dw.com/p/Bu4d

Shari’ar an kammala ta ne da hayaniya tare da cece-kuce daidai yadda aka faro ta misalin watanni 20 da suka wuce. Jim kadan bayan da alkalin da ya shugabanci zaman shari’ar ya fara karanto dalilan hukuncin da aka yanke, nan take daya daga cikin fursinonin mai suna Al-Dagma ya tunkude daya daga cikin jami’an tsaron dake gadinsu gefe guda ya fice daga zauren shari’ar yana mai ihu da cewar tuntuni muka ji wadannan kalamai ba lalle sai an rika maimaita su ba. Sai da aka yi amfani da karfin hatsi domin kakaba masa ankwa, amma duk da haka ya ci gaba da hayaniya har sai da aka fid da shi daga zauren shari’ar baki daya. Shi dai Al-Dagma, wanda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari, ana zarginsa ne da laifin amfani da sunan ‚Al-Tawhid, domin mara wa kungiyar ‚yan ta’adda baya a nan Jamus. Kazalika an same shi da laifin taimaka wa kungiyar da makamai da kuma samar da takardun fasfo na jabu. Sauran fursinoni su uku sun fuskanci hukunci mai tsananin gaske saboda kasancewarsu ‚ya’yan wannan kungiyar ta’adda. An yanke wa fursuna Isma’il daurin shekaru shida, sannan Ashraf shekaru bakwai da rabi sai kuma madugun kungiyar Abu Dhess mai daurin shekaru takwas a gidan kurkuku. Alkalan sun zartar da wannan hukunci ne bisa zargin fursinonin da biyayya ga umarnin madugun ‚yan Ta’adda Al-Zarkawi, wanda ake nemansa ruwa a jallo a sassa daban-daban na duniya. Sun sadu da Al-Zarkawi wajen samun horo na kungiyar al-ka’ida, kuma daga bisani ya rika ba su umarni ta wayar tarfo. Jami’an leken asirin Amurka ne suka sanar da mahukuntan Jamus game da abin dake faruwa. An cafke su a cikin watan fabarairun shekara ta 2002 saboda fargabar yunkurinsu na kai hare-haren ta’addanci. Amon sautin tarfo dinsu da mahukunta suka rika tacewa ya nuna cewar niyyarsu ce su kai farmaki kann kafofi na Yahudawa a Jamus, abin da ya hada har da gidan ibadarsu dake Berlin da kuma wani gidan rawa a birnin Düsseldorf. A baya ga amon sautin na tarfo alkalan kotun sun kuma saurari shaida daga wani da ake kira Schadi Abdallah. Shi ma Abdallah yana daya daga cikin fursinonin da aka cafke, amma bisa sabanin wadancan fursinonin ya fito fili ya hakikance da laifin da ake zarginsan da aikatawa.