1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN YANKA TA TASHI A KASAR IRAQI.

Mansour Bala BelloAugust 16, 2004
https://p.dw.com/p/BvhJ

Wani sabon rikicin ya dada barkewa a can garin najaf na kasar iraqi,bayan kwanaki biyu ana kokarin sasantawa a tsakanin shiawan da kuma sojin amurka.

A yayin da ake wannan sasantawa tsakanin gwamnatin kasar da kuma shugaban shiawan Muqtadr Sadr ne,wasu shiawa suka harbe wasu sojin amurka guda uku,wanda kuma hakan ya sake haifar da wani sabon rikicin.

Ya zuwa yanzu dai sai karar harbe harben bindigogi da kuma tashin boma bomai ake ji a wannan gari.inda har wani bomb da sojin amurka suka harba ya rushe katangar makabartar sayyadina Ali,inda wasu shiawan ke a boye.

A jiya lahadi yan sandan iraqi,sun bukaci duk wasu yan jarida dake cikin garin na najaf dasu bar wannan gari,bisa dalilinsu na cewa babu wani tabbataccen tsaro da zaa iya basu,musamman ma ganin cewa wani dan jarida daya ya rasa ransa wasu biyu kuma sun samu raunuka sakamakon wannan rikici.

A birnin bagadaza dai gwamnatin kasar na gudanar da wani babban taro don samar da yan majalisar dokoki na kwarya kwarya,ana kuma sa ran gwamnatin zata tura wakilanta zuwa garin najaf don tattaunawar sulhu da shugaban shiawan Muqtadr Sadr.

Prime ministan kasar mai rikon kwarya Iyad Allawi,ya kara yin kira ga shiawan dasu yi hanzarin ajiye makamansu,don yin hakan a cewarsa shine kawai zai kawo karshen wannan rikici da ake tayi har kusan makwanni biyu.

Sai dai mai magana da yawun shugaban shiawan Sheik Ahmed Shaibani,ya bayyana cewa ko kusa baza su ajiye makaman nasu ba kamar yadda prime ministan ya bukace su dayi.

Amma kamar yadda ya cigaba da cewa a shirye suke su hau teburin sulhu da wakilan da gwamnatin kasar zata tura najaf,haka kuma a shirye suke dasu tsaya kann kafafuwansu su cigaba da yakar sojin amurka har sai an cimma wata kyakkyawar yarjejeniya.

Can kuma a baquba garin dake arewacin birnin na bagadaza,wasu boma bomai uku ne suka tashi kusa da wani sansanin sojin amurka,wadannan boma bomai sun yi sanadiyyar mutuwar wata yarinya da kanin ta dan shekara shida sakamakon rusa gidansu da bomb din yayi.

Sai kuma wasu jamian kasar iraqin uku dasuka samu raunuka sakamakon tashin wani karamin bomb yayin da motarsu ke kokarin shiga garin baquban.

Kasar iran kuwa har yanzu na gargadi ga kasar iraqi bisa garkuwa da wani jamiinta da akayi a kasar.tare da barazanar har sai iran din ta sako wasu yan iraqi da take tsare dasu tun lokacin yakin iraq da iran wanda ya faru daga shekara ta dubu daya da dari tara da tamanin zuwa shekara ta dubu daya da dari tara da tamanin da takwas.