An yabawa shugaba Musharraf dangane da soke shirin sayen jiragen saman yaki
November 5, 2005Mai kula da ayyukan jin kai na MDD a kasar Pakistan, Yan Vandermoortle ya yaba da shawarar da shugaba Pervez Musharraf ya yanke ta soke shirin sayen jiragen saman yaki daga Amirka. Jami´in na MDD ya ce wannan mataki zai ba da damar sakin kudaden da ake bukata wajen ba da agaji ga wadanda suka tsira daga mummunar girgizar kasar da aka yi a kudancin Asiya a cikin watan jiya. Kafofin yada labaru sun ce Pakistan ta yi shirin sayen jiragen saman yaki samfurin F-16 guda 25, akan kudi dala miliyan 25 ko-wane daya. Vandermootle ya ce yanzu haka dai an kai tantuna da dama don taimakawa mutane sama da miliyan 3 da suka rasa gidajen su sakamakon girgizar kasar. To amma ya kara da cewa har yanzu ana bukatar gas da kananzir da murafu don taimaka musu su rayu a lokacin matsanancin sanyin hunturu. Sama da mutane dubu 73 suka rasu a girgizar kasar wadda karfinta ya kai awo 7.6 a ma´auni Richter.