1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yaba da mutunta dakatar da bude wuta a kasar Yemen

Salissou BoukariApril 11, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da yadda bangarorin da ke gaba da juna a Yemen ke mutunta yarjejeniyar tsagaita buda wutan da aka cimma.

https://p.dw.com/p/1IT3G
Jemen Kämpfer auf einem Toyota Pick up Patrouille
Hoto: picture-alliance/dpa/Stringer

Mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin kasar Yemen Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya yaba da yadda bangarorin da ke fafatawa da juna a kasar suke mutunta yajejeniyar dakatar da buda wutar da ta soma aiki: Ya yi kira ga bangarorin kasar, da kasashen duniya da su bada goyon baya na ganin wannan mataki ya ci-gaba.

Bangarorin da ke gaba da juna a kasar ta Yemen sun sha alwashin mutunta wannan yarjejeniya ta dakatar da bude wuta, inda ake sa ran soma tattaunawa a ranar 18 ga wannan wata na Afrilu muddin dai aka tafi a haka.