An watse baran-baran a taron ƙoli tsakanin EU da Russia | Labarai | DW | 19.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An watse baran-baran a taron ƙoli tsakanin EU da Russia

An watse baran-baran, a taron da ya haɗa shugabar gwamnatin Jamus, bugu da ƙari shugabar ƙungiyar gamaya turai,Angeller Merkel, da shugaban ƙasar Russie Vladmir Poutine.

A ranar jiya tawagogin 2, su ka shirya wannan taron ƙoli, a ƙasar Russia, da zumar fahintar juna, a game da wasu batutuwa da su ka shafi cinikaya da diplomatia, tsakanin Russie, da ƙungiyar gamaya turai.

Saidai bayan yini guda ana tabkka mahaurori, taron bai cimma wani abun a zo a gani ba.

Russia na zargin EU da ɗaurewa wasu ƙasashe membobin ta gidi ,da su ka haɗa da Poland da Lituania.

Cemma manazarta sun ce,“ mun san rina“ ta la´akri ga babban giɓin rashin fahinta da ya shiga tsakanin ɓangarorin 2.

Itama shugabar ƙungiyar EU Angeler Merkel,ta bayyana shakku kamin fara taron, a game da sakamakon da zai haifar.

Saidai Russia da EU ,sun alƙawarta ci gabada saduwa akai akai, har sai sun cimma tundun dafarwa.