An watsa faifayen bidiyo na mataimakin shugaban al-Qaida al-Zawahiri | Labarai | DW | 29.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An watsa faifayen bidiyo na mataimakin shugaban al-Qaida al-Zawahiri

Mataimakin shugaban kungiyar al-Qaida Ayman al-Zawahiri yayi ikirarin cewa hare haren kunar bakin wake da suke kaiwa ya karya lagon sojin Amirka a Iraqi. a cikin wani faifayen bidiyo da aka saka cikin shafin intanat na wata kungiyar Islama, al-Zawahiri ya kuma yi Allah wadai da shugabannin Masar, Jordan, Saudiyya da kuma Iraqi da cewa maciya amanar ne kuma yayi kira ga al´umar musulmi da su tayar musu da kayar baya. Bidiyon na baya bayan nan ya zo ne kwnaki kalilan bayan wani caset da aka watsa na shugaban al-Qaida Osama Bin Laden da kuma bidiyon shugaban kungiyar a Iraqi Abu Musab al-Zarqawi.