1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An wanke soja guda da ake zargi da laifin azabtar da fursunonin Abu Ghraib

January 11, 2008
https://p.dw.com/p/CoVb

Hukumomin soja a ƙasar Amurka sun wanke jami’in soji guda da ake zargi da azabtar da fursunonin gidan yarin Abu Ghraib a ƙasar Iraƙi. Laftanar kanar Steven Jordan shike ke shuganacin harkokin gidan yarin a lokacinda aka dauki hotunan yadda ake azabtar da fursunonin a 2003.A watan Agusta kuma aka wanke shi daga laifin wulaƙanta fursunonin,amma kuma an kama shi da laifin yin watsi da dokar da ta hana shi tattaunawa kan bincike da akeyi,yanzu haka kuma anyi watsi da wannan zargi wanda hakan ya ɓata rayukan masu yakuwar kare hakkin bil Adama. Sun ce rundunar sojin Amurkan ta gagara gudanar da bincike kan wasu manyan jami’anta da suke da hannu cikin batun azabtar da fursunan Abu ghraib duk da alkawarin yin hakan da suka yi.