An wanke kwamandan Jamus a harin Afganistan | Labarai | DW | 20.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An wanke kwamandan Jamus a harin Afganistan

Rundunar sojin Jamus ta wanke Kanal Klein game da harin Kunduz wanda ya halaka fararen hula fiye da 100

default

Kanal Georg Klein

Hukumomin Sojin Jamus sun wanke wani tsohon kwamandan Sojin ƙasar a Afganistan, wanda ya bada umarnin kai hari akan wasu tankunan mai da 'yan Taliban suka sace wanda kuma ya halaka Afganistawa fiye da ɗari a yankin Kunduz.

Ma'aikatar tsaron Jamus tace zata dakatar da binciken da takeyi akan Kanal Georg Klein, bayan da binciken farko ya gano cewar bashi da laifi wajen aika laifi. A watan Afirulun bana ne dai, masu binciken gwamanati suma suka yi watsi da wannan zargi da akewa Sojan, bisa hujjar cewar bai karya dokokin ƙasa da ƙasa ba.

Harin ta ranar 4 ga watan Satumban bara ta haifar da kace nace tsakanin hukumomin tsaron NATO da kuma gwamnatin Afganistan da kuma 'yan adawa anan Jamus sakamakon fararen hulan da aka halaka su feye da ɗari.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed Abubakar