1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tuna da Anna Politkowskaya a birnin Mosko shekara guda bayan kisan ta

Masu fafatukar kare hakin bil Adama da ´yan adawa a Rasha sun yi bukin tunawa da cika shekara daya da kisan gillar da aka yiwa ´yar jaridar na mai sukar lamirin fadar Kremlin Anna Polikowskaya. A karkashin tsauraran matakn tsaro daruruwan mutane ne suka hallara a birnin Mosko a gun taron gangami da aka yi don tunawa da ´yar jaridar. Sun yi tir da manufofin take hakin ´yan jarida sannan sun yi kira ga gwamnati da ta fadi gaskiya a dangane da kisan wamda ya auku a ranar 7 ga watan oktoban shekara ta 2006. Ita dai Politkowskaya ta yi ta buga rahotanni game da take hakin bil Adama a Chechniya.