An tuhumi sojojin Amirka biyu da yiwa ´yan Iraki 3 kisan gilla | Labarai | DW | 30.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tuhumi sojojin Amirka biyu da yiwa ´yan Iraki 3 kisan gilla

Rundunar sojin Amirka ta ce dakarun ta da na Iraqi sun kashe ´yan tawaye 26 a wani samame da suka kai a birnin Bagadaza da asubahin yau asabar. Rundunar ta zargi mutanen da alaka da kungiyoyin ´yan ta´adda na Iran. To amma mazauna yankin sun ce dukkan wadanda aka kashen fararen hula ne wadanda ba su san hawa ba su san sauka ba. A wani labarin kuma rundunar sojin Amirka a Iraqi ta ce ta caji sojojin ta biyu da yiwa wasu ´yan Iraqi su 3 kisan gilla a Iskandariyya dake kudu da birnin Bagadaza. Rundunar ta ce an aikata kisan ne daga watan afrilu zuwa yuni. Bayan kisan sojojin sun dora makamai akan gawawwakin don nuna cewa wadanda suka kashen ´yan tawaye ne. Yanzu haka dai ana tsare da sojojin a wani kurkun sojin Amirka dake kasar Kuwaiti kafin su gurfana gaban kotu.