An tuhumi sojin Amirka biyu da ganawa firsinonin Afghanistan azaba | Labarai | DW | 30.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tuhumi sojin Amirka biyu da ganawa firsinonin Afghanistan azaba

An tuhumi sojin Amirka biyu da laifin cin zarafin firsinoni a Afghanistan, inji rundunar sojin Amirka a birnin Kabul. Hakan dai ya zo ne mako guda kacal bayan an zargin dakarun Amirka da kone gawawwakin mayakan kungiyar Taliban. An tuhumi sojojin ne a karkashin dokar soja da laifin ganawa mutane biyu da suke tsare da su azaba a lardin Uruzgan dake kudancin Afghanistan. A makon da ya gabata al´umar Afghanistan sun nuna kaduwa bisa hotunan da wata tashar telebijin Australiya ta nuna na wasu sojin Amirka suna kona gawawwakin mayakan kungiyar Taliban, wanda haka ya sabawa dokokin kasa da kasa da kuma shari´ar addinin musulunci wadda ta tanadi binne gawar musulmi. Rahoton ya ce an kone gawawwakin ne saboda an bar su a waje har tsawon sama da sa´o´i 24. To sai dai sun yi amfani da haka don tsokanar wasu ´yan Taliban.