1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsinci gawar ɗaya daga cikin Jamusawa biyu da aka garkuwa da su a Afghanistan

A ci-gaba da neman ´yan kasar KTK 23 da ake garkuwa da su dakarun Afghanistan da na Amirka sun yiwa wani kauye dake lardin Ghasni kawanya. Wani kakakin ma´aikatar tsaro a birnin Kabul ya ce an san wurin da aka boye mutanen da ake garkuwar da su. A kuma halin da ake ciki an tsinci gawar daya daga cikin Jamusawa biyu da aka yi garkuwa da su a kudancin Afghanistan. Tun dai a jiya ´yan kungiyar Taliban sun ce sun harbe mutanen biyu har lahira bayan da gwamnatoci a Kabul da Berlin suka ki tuntubar ´yan tawayen. Ministan harkokin wajen Afghanistan Rangin Dadfar Spantan yayi tir da garkuwa yana mai cewa.

Spantan:

“Wannan wani aiki ne na dabbanci wanda muke Allah wadai da shi. Al´umar Afghanistan na nuna zumuncin su ga iyalan wadanda abin ya shafa.