1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: An saka ranar zabe

Usman Shehu Usman RGB
May 31, 2018

Ranar 30 ga watan Yulin da ke tafe ita ce ranar da mahukuntan kasar Zimbabuwe suka tsayar a matsayin ranar zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki amma talakawan kasar da ke zama a ketare suna cikin damuwa.

https://p.dw.com/p/2yiK3
Burundi Verfassungsreferendum
Hoto: Imago/Xinhua/E. Ngendakumana

A cewar wakilin DW da ke birnin Harare, wannan sanarwar da gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa ta fitar a jiya Laraba, kusan babu wata murna a bangaren talakawan kasar ta Zimbabuwe dake zama a ketare domin kuwa basu da damar kada kuri'a bisa dokokin kasar duk kuwa da samun sauyin gwamnati.

SADC Gipfel Proteste
'Yan Zimbabuwe dake zama a ketare sun baiyana damuwa kan dokar hana su damar kada kuri'a.Hoto: picture-alliance/ dpa

Wani hukuncin da kotun kolin kasar ya yanke a yammacin jiya Laraba, shi ne ya haramtawa daukacin 'yan kasar Zimbabuwe mazauna ketare kada kuri'a, har sai lokacin da aka yi wa dokokin zaben kasar kwaskwarima. Kawo yanzu dai a hukumance babu yawan alkaluman 'yan kasar Zimbabuwe da suke tsere daga kasar izuwa kasashen ketare sakamakon matsalolin siyasa da na tattalin arziki, amma ana kiyasin sama da 'yan Zimbabwe miliyan biyu ne ke zama a kasashen waje.

Simbabwe Volksentscheid zur neuen Verfassung
A watan Yulin 2018 za a gudanar da babban zaben kasar ZimbabuweHoto: Reuters

Shugaba Mnangagwa zai fafata da dan takarar babbar jam'iyar adawa ta MDC Nelson Chamisa wanda matashi dan shekaru 40. Kawo yanzu dai ba a san dalilan da suka sa aka hanawa 'yan kasar da ke zama ketare 'yancin yin zabe ba to amma akasarin jama'a rayoyinsu sun karkata kan cewa babban dalilin shi ne mafi yawan 'yan Zimbabuwe da ke zama a kasashen waje sun fi alaka ne da jam'iyar adawa.