An tsawaita zabe a wasu sassan Jamhuriyar Nijar
February 22, 2016Talla
Ana ci gaba dakon sakamakaon zaben kasar Jamhuriyar Nijar wanda aka tsawaita a wasu sassa na kasar. Tuni kungiyar Tarayyar Afirka ta nuna gamsuwa da yadda zaben ke gudana a kasar da ke yankin yammacin Afirka.
Tuni 'yan adawa suka yi gargadi kan bisa cewa Shugaba Mouhamadou Issougou da ke neman wa'adi na biyu na mulki ya guje wa duk wani yunkuri na magudi domin samun nasara a zagayen farko na zaben.
Bisa tsarin kasar dan takara zai samu nasara a zagayen farko idan ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada, idan babu wanda ya samu wannan adadi sai a tafi zagaye na biyu na zabe.