An tsaurara matakan tsaro a Burkina Faso | Labarai | DW | 09.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsaurara matakan tsaro a Burkina Faso

Gwamnatin Burkina Faso ta tsaurara matakan tsaro don yaƙi da ta'addanci.

default

Shugaba Blaise Compaoré.

Gwamnatin ƙasar Burkina Faso ta ba da sanarwar ƙara ƙarfafa matakan tsaro,sakamakon barazana ta ta'addanci da yankin yammaci Afrika ya ke fama da shi. Ko da shike hukumomin sun tabbatar da cewa babu wani abin fargaba akan sha'anin tsaro, to amma sun ce za su tanadi matakai na ko ta kan ƙwana, domin fuskantar duk wata barazana ta 'yan ta'addar da ka iya tasowa. Wannan shela dai ta biyo bayan gargaɗin da ƙasar Faransa ta yi ne ga 'yan ƙasarta da ke zaune a ƙasar da cewa su yi hattara, sannan kuma da janyewar Amirkawa da dama a cikin ƙwanakin na baya baya nan daga arewacin ƙasar wato a garuruwan da ke kan iyaka da ƙasashen Niger da Mali, inda aka ba da rahoton cewa reshen ƙungiyar al-Ƙa'ida na Aqmi na girkuwa da sannu a hankali.

Mawallafi: Abdourahamane Hassan

Edita: Halima Balaraba Abbas