1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsare ’yan majalisar ƙungiyar Hamas a birnin Ƙudus.

A wata sabuwa kuma, ’yan sandan Isra’ila sun tsare wasu ’yan majalisan ƙungiyar Hamas guda uku a birnin ƙudus yau da safen nan, sabooda zargin da suke yi musu na shiga cikin wata zanga-zangar da aka haramta, a wuraren ibada masu tsarki na birnin. Wata sanarwar da ’yan sandan birnin suka bayar ta ce, an kai ’yan majalisar, Mohammed Abu Teir, da Ahmed Abou Atoum da Khaled Abu Arafa a wani kurkukun birnin ne, inda aka yi musu tambayoyi game da zargin da ake yi musu. Dukkan ’yan majalisar dai na zaune ne a yankin na birnin Ƙudus. Ɗaya daga cikinsu, Abu Arafa, shi ne kuma ministan da ƙungiyar Hamas ɗin ta naɗa mai kula da harkokin birnin Ƙudus.

Ya faɗa wa maneman labarai cewa, tun da ƙarfe shida na safiyar yau ne ’yan sandan suka ɗauko shi daga gidansa, suka yi ta masa tambayoyi har tsawon sa’o’i da dama. Ana zarginsa ne da shirya zanga-zangar da aka yi a masallacin al-Aqsa a ran juma’ar da ta wuce, inda aka bukaci jama’a da su ba da gudummowa ga gwamnatin Falasɗinawa ta ƙungiyar Hamas, wadda a halin yanzu, saboda takunkumin da ƙasashen Yamma da Isra’ila sukka sanya mata, ke huskantar munanan matsaloli na rashin kuɗi.