An tsare wata mai sukar Shugaba Kagame | Labarai | DW | 04.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsare wata mai sukar Shugaba Kagame

'Yan sanda a Ruwanda sun kama wata fitacciyar 'yan siyasar kasar Diane Shima Rwigara, wadda aka harantawa takara da shugaba Paul Kagame na kasar a zaben kasar.

'Yan sanda a Ruwanda sun kama wata fitacciyar 'yan siyasar kasar Diane Shima Rwigara, wadda aka harantawa takara da shugaba Paul Kagame na kasar. Ita dai wannan 'yar siyasar wadda kuma ta yi kaurin suna da fafutuka, ta shiga hannu ne tare da mahaifiyarta da ma wata 'ya uwarta ta jini, saboda zarginsu da ake yi da kin biyan haraji da kuma amfani da wasu takardu na boge.

Rundunar jami'an 'yan sandan kasar ta ce 'yar siyasar na fuskantar zargin amfani da takardun na boge ne, a musamman cikin takardun da ta bayar na neman takarar shugabancin kasar da aka yi a watan jiya. Ita ma dai hukumar zaben kasar ta kafa hujjar soke sunan 'yar siyasar ne, da yin amfani da sa hannun karya gami da amfani da sunayen wasu da aka ce tuni suka riga suka mutu, sai dai fa ta musanta wadannan zarge-zargen.