An tsare wani wanda ke neme ruwa a jallo a Saudiya | Labarai | DW | 27.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsare wani wanda ke neme ruwa a jallo a Saudiya

Wasu yan sandan kasar Saudiyya su 5 sun rasa rayukansu a lokacinda wani dan bindiga dadi wanda jamian tsaro suka ce yana daya daga cikin mutane 36 da Saudiyyan take nema ruwa a jallo ya bude wuta a kansu.

Wata sanarwa daga ofishin harkokin cikin gida ta Saudiyyan tace tuni an tsare mutumin mai suna Muhammad bin Abdulrahman al Suweilimi wanda aka ce yana da alaka da kungiyar Al-Qaeda.

Ana zargisa kuma da laifin kashe wasu yan sanda biyu a yankin Buraida.

Rahotanni sun baiyana cewa Suweilimi kwararre a fannin ilmin sadarwa ta internet, ya taimakawa kungiyar ta Al-Qaeda mika sanarwa ta hanyar yanar gizo.

Sanarwar ta kara da cewa Suweilimi ya samu rauni alokacin tsare shi.

Kasar Saudiyya wadda itace mahaifar Osama bin laden,tana fama da hare hare daga magoya bayan Al-Qaeda,shekaru biyu yanzu,hari na baya mafi girma ya faru ne shekara guda da ya gabata,kuma tun daga wancan lokaci jamian tsaro sun kashe da yan gwagwarmaya da dama.

A wani labarin kuma a saudiyan,a yau din nan aka fiile kan wani dan kasar Sudan da aka kama da laifin kashe dan uwansa dan sudan ,wanda hakan ya kawo yawan wadanda aka kashe a saudiya zuwa 8 cikin wannan wata.

An dai kama Muhammad Nur Ali da laifin dukkan Ali al-fadel al-Nur da karfe tare da yanke masa makogoro bayan wata yar takaddama da ta tashi tsakaninsu.

Cikin wannan shekara kasar saudiya ta kashe masu laifi 82 .

Karkashin dokar kasar ana yanke hukuncin kisa akan masu laifuka da suka hada da,kisan kai,fyade,ridda,fashi da makami da kuma safarar miyagun kwayoyi.