An tsare wani jamiin leken asirin Sudan a Jamus | Labarai | DW | 23.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsare wani jamiin leken asirin Sudan a Jamus

Hukumomi anan Jamus sun tsare wani jamiin leken asiri na kasar Sudan wanda ake zargi yana kai rahotannin harkokin magoya bayan yan adawa na Sudan dake zaune anan Jamus ga hukumar leken asiri ta Sudan.Ofishin babban alakali na gwamnatin Jamus yace jamiin dan shekaru 39 da haihuwa an tsare shi ne a birnin Berlin a karshen mako,amma sai yau aka sanarda tsare shi.Ana ganin cewa tun ranar 1 ga watan yuli na 2005 jamiin yake aiyukan leken asiri a nan Jamus.