1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsare sojojin Jamus kan zargin tsaro

Usman Shehu Usman
May 10, 2017

A kasar Jamus wata sabuwar muhawara kan rundunar sojin kasar ta dauki sabon salo, bayan kara tsare wasu sojoji guda uku bisa tuhumarsu da shirya kai harin ta'addanci.

https://p.dw.com/p/2cjXz
Frankreich  Illkirch-Graffenstaden Bundeswehr Soldaten vom Jägerbataillon 291
Hoto: Getty Images/AFP/F. Florin

Wannan batun samun sojoji a rundunar sojin Jamus, wadanda suke shirin aikata ta'addanci zai kansance babbar muhawara daf da lokacin da kasar ke shirin gudanar da zaben kasa. Tun kama sojin farko 'yan adawa suka fara aza ayar tambaya bisa matsayin tsaro a Jamus. Don haka ake sa ran ministan tsaron kasar ta Jamus Ursula von der Leyen, za ta bayyana gaban majalisar dokokin don amsa tambayoyi kan wannan babban barazanar tsaro da aka bankado.

Frauke Koeler ita ce mai magana da yawun ofishin babban mai gabatar da kara a Jamus, ta kuma yi karin haske bisa tsare sojojin da aka yi a jiya. "A bisa bincikenmu kawo yanzu, mun kama  sojojin uku da muka tsare, suna shirin kai harin don halaka wasu manyan 'yan siyasa da fitattun, wadanda ke taka muhimmiyar rawa, kamar yadda masu kitsa harin suka bayyana cewar suna zargin mutanen ne da yaudarar Jamus wajen tsarin karbar 'yan gudun hijira da baki."

Masu yin  bincike a cikin barikokin soji na Jamus sun bayyana cewar daga cikin sojoji ukun da aka kama, sun gano cewar wadannan kuratan sojoji sun yi nisa da shirinsu na kai harin ta'addanci, kuma sun dau matakai na gaske wanda da wuya hukuma ko 'yan uwan su sojoji su gane abin da ake shirin yi.