An tsare shugaban Khmer Rouge | Labarai | DW | 19.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsare shugaban Khmer Rouge

Rahotanni daga kasar cambodia sunce an tsare wani babban jamiin kungiyar Khmer Rouge.Nuon Chea dan shekaru 82 da haihuwa shine babban shugaban kungiyar da yake raye,an kuma tsare shine bisa zargin cewa shine ya kirkiro da manufofi na kashe kashen abokan adawa na gwamnati.Jamian kasar Cambodia sunce rundunoni na musaman da suka hada da yan sanda da sojoji sunyiwa gidan Nuon kawanya .Akalla mutane miliyan daya da dubu dari bakwai aka kiyasta an kashe a shekarun 1970.