An tsare Khaleda Zia | Labarai | DW | 03.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsare Khaleda Zia

Yan sanda a babban birnin kasar Bangladesh Dhaka sun tsare tsohuwar firaminista Khaleda Zia da danta bisa zargin cin hanci da rashin iya gudanar da aiki.Wadanda suka ganewa idanunsu sunce jamian yan sandan sun tsare su ne a gidansu dake Dhaka jim kadan bayan wani jamiin hukumar yaki da cin hanci na kasar ya shigar da kara akansu.rahotanni sunce an kai su zuwa babbar kotun birnin.Zargi da ake musu dai ya hada da batutuwan bada kwangila ga wadanda basu cancanta ba a lokacinda mulkinta da ya kare a watan oktoba.Gwamnatin rikon kwarya wadda take da goyon bayan soji ta kaddamar yaki da cin hanci da Rashawa bayan kwace darewa mulkin kasar a watan janairu.Daya tsohuwar firaministar kasar Sheikh Hasina tana tsare tun bayan wani caji da aka mata itama na cin hanci da rashawa.