An tsare dan fashin jirgin saman Sudan | Labarai | DW | 24.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsare dan fashin jirgin saman Sudan

Jamian tsaro sun tsare dan bindiga da yayi fashin wani jirgin saman kasar Sudan yayinda jirgin ya sauka a birnin N’djamena na kasar Chadi.

Mutumin ya mika kansa ba tare da wata matsala ba kuma rahotanni sunce dukkanin fasinjoji 103 dake jirgin babu abinda ya same su.

Jirgin ya tashi ne a safiyar yau daga birnin Khartoum zuwa birnin Al-Fasher dake yammacin Sudan,yayinda dan bindigar ya tilastawa matukin jirgin sauya akalarta zuwa kasar Chadi.

Wani jamiin kanfanin jirgin da kuma wani minista na kasar Chadi sunce dan bindigar yace yana neman mafaka ne a kasar Burtaniya.