An tsananta binciken neman bakar akwatu a Nigeria | Labarai | DW | 24.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsananta binciken neman bakar akwatu a Nigeria

Rahotanni da suka iso mana daga Nigeria na nuni da cewa har yanzu ana nan ana ci gaba da laluben bakar akwatun nan dake kunshe da bayanai a cikin ta a kusa da lissa inda jirgin saman kamfanin belview yayi hatsari a ranar asabar din data gabata.

Wannan dai bayani daya fito daga bakin ministan ma´aikatar kula da sufurin jirgin sama ya kawo sabani da bayanin farko daya fito daga bakin kwamishinan yan sanda Tunji Alapini.

Idan dai za a iya tunawa a can baya kamfanin dillancin labaru na AFP ya rawaito kwamishinan yan sandan na fadin cewa jami´ansu sun tsinto bakaken akwatunan jim kadan bayanan bayyanarsu a gurin da akayi wannan hatsari.

Wannan dai bakar akwatu a cewar rahotanni na dauke da bayanai ne na dukkannin abubuwan dake faruwa a tsakanin matukan jirgi da kuma hasumiyar kula da zirga zirgar jiragen sama.