1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsaida ranar zaɓe a ƙasar Cote D´Ivoire.

Yahouza, SadissouApril 15, 2008

Zaɓen shugaban ƙasar Cote d`Ivoire 30 ga watan Nowember na shekara ta 2008.

https://p.dw.com/p/DiXE
Gwamnati ta tsaida ranar zaɓen shugaban ƙasa a Cote d`IvoireHoto: AP


Gwamnatin ƙasar Cote d`Ivoire ta tsaida ranar 30 ga watan Nowemba na shekara da muke ciki, a matsayin ranar zaɓen shugaban ƙasa zagaye na farko.

A jiya ne, kakakin gwamnatin Cote d`Ivoire,Amadou Kone ya bayyana wannan sanarwa, bayan taron Majalisar Ministoci na mussamman da Framinista Guillaume Soro ya jagoranta.

A cewar sanarawar, hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta shawarci gwamnati ya tsaida ranar zaɓen shugaban ƙasa a 30 ga watan Nowemba.

Nan gaba Hukumar za ta bayyana lokacin da za ta fara rijistan ´yan takara a zaɓen.

A wani taron manema labarai da ya kira shugaban ƙasar Cote D´Ivoire Lauran Bagbo, ya dangata ranar ta jiya, a matsayin rana ta tarihi, ta la´akari da matakin da gwamnati ta ɗauka, bayan shekaru kussan ukku ana tafka mahaurori a game da shirya zaɓen.

Bagbo, da zai tashi a yau zuwa fadar Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York na Amurika, yayi kira ga hukumar dake kula da shirya katinan zaɓe da dukkan sauran masa ruwa da tsaki a cikin wannan al´amari su ɗauki matakan da suka dace, ta yadda zaɓen zai wakana lau lami.

A nasa gefe, ya alƙawarta bada haɗin kan da ya dace.

Da farko, a watan october na shekara ta 2005 ne, aka buƙaci gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, amma aka dage shi har sau uku, ta la´akari da ƙiƙi-ƙaƙar da ake samu tsakanin ɓangarorin masu gaba da juna.

An cimma yarjeniyar zaman lahia, tsakanin gwamnati da ´yan tawaye a watan Maris na shekara ta 2007 a birnin Ouagadougou na Burkina Faso, wace a sakamakon ta, magudun ´yan tawaye Guillaume Soro ya zama Framinista.

Yarjejeniyar ta tanadi ´yan tawayen su kwance ɗamara yaƙi, bayan wata da watani na taci bataci , sai a ranar lahadin da ta wuce suka cika wannan umurni.

A ɗaya waje,n yarjejiyar Ougadadoudou ta tanadi rijistan jama´a, tare da basu takardun zama ´yan ƙasa.

A cewar wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar Cote D´ivoire ya zuwa yanzu, kotunan ƙasar sun yiwa a ƙalla mutane dubu ɗari biyar rijista.

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon, ya bayyana matuƙar gamsuwa da ci gaba da aka samu ta fannin shirya zaɓe a ƙasar D´Ivoire, ya kuma alƙawarta kai ziyara ƙasar a cikin wannan wata domin ƙara ƙarfin gwiwa ga hukumomi.