An tattauna tsakanin Bush da Abbas | Labarai | DW | 20.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tattauna tsakanin Bush da Abbas

Bayan ganawar da suka yi da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a birnin Washington, shugaban Amirka GWB ya ce dole ne hukumar mulkin cin gashinkan Falasdinawa ta murkushe kungiyoyin ´yan takife, idan ana son a cimma zaman lafiya a yankin GTT. Bush ya kuma ce dole ne Isra´ila ta dakatar da gina matsugunan Yahudawa ´yan kakagida, sannan Amirka zata ba da tata gudummawa wajen ganin an zauna kan teburin shawarwari tsakanin Isra´ila da Falasdinawa. To sai dai Bush ya ki ba da wani tsarin lokaci game da wanzar da zaman lafiyar GTT sannan ya ki ya ba da tabbaci akan kafa wata ´yantacciyar kasar Falasdinu gabanin ya sauka daga kujerar shugaban Amirka a watan janerun shekara ta 2009. Shi kuwa a nasa bangaren Abbas yayi kira ga isra´ila da ta daina gina matsugunan yahudawa a yankunan Falasdinawa tare da tsayar da aikin gina katangar nan a Gabar Yammacin kogin Jordan. Abbas ya jaddada cewa yanzu lokaci yayi da za´a ciyar da shirin wanzar da zaman lafiya na taswirar hanya gaba.