An tashi taron kungiyar WTO ba da wani sakamako | Labarai | DW | 01.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tashi taron kungiyar WTO ba da wani sakamako

A birnin Geneva, an katse zaman taron kasashen kungiyar cinikaiya ta duniya WTO a game da sakarwa harkokin kasuwanci mara ba tare da wani sakamako ba. Kwamishinan ciniki na kungiyar tarayyar Turai Peter Mandelson yayi gargadi game da rushewar yarjejeniyar ciniki ta birnin Doha. Shi kuwa a nasa bangaren ministan cinikaiya na Indiya Kamal Nath ya bayyana taron da cewa ya watse kuma babu wata alamar ceto shi. To sai dai shugaban kungiyar WTO Pascal Lamy ya ce har yanzu da akwai damar cimma wata yarjejeniya a cikin makonni masu zuwa. Yarjejeniyar Doha, wato babban birnin Qatar, wadda ta fara aiki a cikin shekara ta 2001 ta tanadi kawad da kariyar da ake ba wa kamfanoni, wadda ke tarnaki ga huldar ciniki ta duniya.